Liverpool za ta kasance cikin shiri wajan sauraron tayin sayan dan wasan gabanta na Columbia Luis Diaz, mai shekara 27, a bazara idan dan wasan gabanta na Masar, Mo Salah mai shekara 31, ya amince da sabon kwantaragi.
Liverpool za ta bukaci kudi fiye da fam miliyan 100 domin sayar da Salah zuwa ga Saudi Pro League a wannan bazara, a dan haka kungiyar ta yi amannar cewa za ta samu isashen kudin wajen maye gurbinsa a wannan kakar.
Tottenham Hotspur na ci gaba da bibiyar halin da dan wasa tsakiya na Ingila Conor Gallagher ya ke ciki a Chelsea kuma a shirye ta ke ta dauko dan wasan mai shekara 24 a wannan bazara (Daily Mail)
Arsenal na gab da fara tattaunawa da dan wasan tsakiya na Italiya Jorginho, mai shekara 32, a kan sabon kwantaragisa a kunjiyar.
Kocin Brighton Roberto de Zerbi shi ne a gaba -gaba a cikin wadanda za a zaba a matsayin kocinyan Manchester United.
Getafe a shirye ta ke ta fara tattaunawa da Manchester United game da tsawaita zaman Mason Greenwood a kungiyar, ta.
Ita ma Barcelona na son ta ci gaba da rike ‘yan wasan Portugal da aka ba ta su aro watau Joao Cancelo da Joao Felix a kakar wasa mai zuwa kuma a shirye ta ke ta ba Manchester City yuro miliyan 15 zuwa 20 a kan dan wasan baya Cancelo mai shekara 29 da dan wasan gaba Felix mai shekara 24 domin Atletico Madrid ta sake ba da shi aro.
Watakila Chelsea ta dauko mai tsaron ragar Arsenal Aaron Ramsdale mai shekara 25 ,a kasuwar sayar da ‘yan wasa ta bazara.
Dan wasan baya na Ingila Eric Dier mai shekara 30 ya cika sharuddan kwantaraginsa da ake bukata domin ya koma dan wasa na dindindin a Bayern Munich a karshen kakar wasanni. Tottenham ce ta ba da shi aro. (Athletic)
Bayern Munich a shirye ta ke ta biya kusan yuro miliyan 100 don sayan dan wasan bayan Portugal Antonio Silva mai shekara , 20 daga Benfica. (Sport - in Spanish)
AC Milan da Juventus na zawarcin dan wasa mai hari na Moroko Youssef En-Nesyri, mai shekara 26,.

Post a Comment