Top News

An bayyana rahoton cewa Dani Alves ya shaki iskar 'yanci, Alphonso Davies ba zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Bayern ba. A cewar Romano.

A hukumance: An saki tsohon dan wasan Barcelona daga gidan yarin ranar Litinin bayan shafe watanni 15 yana jiran shari’ar sa bisa laifin yi wa wata mata fyade a watan Disambar shekarar 2022.

An samu matashin mai shekaru 40 da laifi a watan Fabrairun wannan shekarar, kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu da rabi, amma Alves na ci gaba da daukaka kara kan hukuncin, kotun.
Alves ya mika fasfo dinsa na Spaniya da na Brazil, kuma zai rika ziyartar kotu sau daya duk mako domin samun 'yancinsa, bayan da ya fara biyan  Yuro miliyan 1.

Alphonso Davies ba zai sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Bayern ba. A cewar Romano

Za a yanke shawara a cikin makonni masu zuwa 

Idan ba a amince da tsawaita kwantiraginsa ba, Davies zai bar wannan bazara.

Real Madrid, ta shirya bude tattaunawa da Bayern Munich. 

Dan wasan baya na Bayern Munich Alphonso Davies yana gab da komawa kungiyar Real Madrid a wannan bazarar. 

Dan wasan na Canada mai shekaru 22, kwantiraginsa zai kare ne a shekarar 2025, kuma yayin da Bayern Munich ke son sabunta kwantiraginsa dan wasan. A halin da ake ciki dai Real Madrid na jira, tana fatan yin amfani da yanayin da ake ciki a bazara, kamar yadda Bayern ta bayyana a fili cewa za ta sayar da Davies idan bai amince da sabon tayin kunjiyar ta Munich ba.
Babu shakka Alphonso Davies yana daya daga cikin mafiya kyawun ‘yan wasan baya na hagu a duniya, kuma Real Madrid tana zawarcinsa tsawon shekara guda.

2 Comments

Post a Comment

Previous Post Next Post