Ɗan wasan tsakiya a Jamus Toni Kroos, mai shekara 34, ya tsawaita zamansa na shekara guda a Real Madrid.
Kociyan Man City Pep Guardiola ya kwaɗaitu da ɗan wasan tsakiya Newcastle Bruno Guimaraes, mai shekara 26, amma dole Manchester City ta kashe yuro mliyan 100 wajen saye dan wasan.
Kunjiyar Arsenal ta jero mutane 10 da take zawarcinsu a wannan kaka ciki harda ɗan wasan gaba a RB Leipzig daga Slovenian Benjamin Sesko, mai shekara 20 da dan wasan Sporting Lisbon Viktor Gyokeres, mai shekara 25, da kuma abokin wasansa a Sweden, Alexander Isak, mai shekara 24.
Manchester United ta matsa kaimi kan ɗan wasan tsakiya na Everton, Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, yayinda suke son inganta bayansu a sabuwar kaka wasanni.
Chelsea na cikin kungiyoyin da ke zawarcin mai tsaron ragar Athletico Paranaense, Bento mai shekara 24, wanda ya haska a fafatarwar Brazail da Ingila a makon da ya gabata.
Tottenham na son saye ɗan wasan Feyenoord da Mexico Santiago Gimenez, mai shekara 22, domin maye gurbin Harry Kane a wannan kakar. Shekara guda bayan da dan wasan mai shekara 30 daga Ingila ya koma Bayern Munich.
Ɗan wasan gaban Liverpool Luis Diaz mai shekara 27, bai cire ran tafiya wata kungiyar Sifaniya domin buga La Liga ba a nan gaba a cewar mahaifinsa.
Manchester United na son saye ɗan wasan baya na Argentine, Aaron Anselmino mai shekara 18 daga Kunjiyar Boca Juniors.
Kocin Brighton Roberto de Zerbi ya kasance wanda Bayern Munich ke son dauko idan har sun gagara dauko Xabi Alonso daga Bayer Leverkusen.
Tottenham da West Ham da Brighton da kuma Everton na shirya yadda kowanne su zai yi nasarar saye ɗan wasan Juventus da Ingila, Samuel Iling-Junior, mai shekara 20.
Ɗan wasan tsakiya a Italiya Jorginho mai shekara 32, na iya bankwana da Arsenal a wannan kaka.
Fatan Arsenal na saye ɗan wasan gefe Xavi Simons mai shekara 20 zai fuskanci kalubale saboda PSG na son ta cigaba da rike shi idan ya dawo daga zaman aro da yake yi yanzu haka a RB Leipzig.
Manchester United za ta amincewa ɗan wasan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 32, ya tafi a karshen kaka.
Ana yada jita-jita kan Real Madrid za ta saye ɗan wasan Liverpool da Ingila, Trent Alexander-Arnold, mai shekara 25.
Mai taimakawa kocin Liverpool Pep Lijnders na iya zama sabon kocin Ajax next a sabuwar kaka.
West Ham na sa rai Manchester City ta sake gabatar da tayi kan ɗan wasan tsakiyar ta na Brazil, Lucas Paqueta mai shekara 26.
Kyakkyawan labari
ReplyDeletePost a Comment