Top News

Man Utd na farautar Dani Olmo da Joselo da Bremer, Lukaku na dab da tafiya Saudiyya

Man United ta shiga sahun masu farautar ɗan wasan Sifaniya Dani Olmo, wanda yarjejeniyarsa a RB Leipzig ke iya ba shi damar tafiya wata ƙungiyar kan fam miliyan 52. Ɗan wasan gefen mai shekara 25 ya ja hankalin ƙungiyoyi irinsu, Real Madrid da Manchester City da Chelsea da Tottenham.


Man United za ta biya akalla yuro miliyan 60 kan ɗan wasan Brazil mai shekara 27, Gleison Bremer, da ke taka leda a Juventus, kuma watakil yarjejeniyar ta kunshi har da miƙa ɗan wasansu,na Ingila Mason Greenwood, mai shekara 22. 

Man City da Newcastle za su kalubalanci Man United kan saye ɗan wasan Everton da Ingila Jarrad Brathwaite, mai shekara 21.

Man United suna farautar ɗan wasa Joselu mai shekara 25 da ke zaman aro a Real Madrid.

Kungiyar Italiya Genoa ta na fatan karban tayi kan ɗan wasanta na gaba mai shekara 26 daga Iceland, Albert Gudmundsson, wadda ake alakantawa da Tottenham da kuma West Ham. 

Chelsea za ta maye gurbin Todd Boehly a matsayin shugaba a 2027.

Crystal Palace na son saye ɗan wasan Valencia mai shekara 19, Cristhian Mosquera a wannan kaka amma tana fuskantar kalubale daga Atletico Madrid.

Akwai kwarin gwiwar ɗan wasan Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 30, da ke zaman aro a Roma daga Chelsea, zai koma Saudiyya.

Manchester United da Tottenham na farautar ɗan wasan Faransa, Jean-Clair Todibo, mai shekara 24, wanda ake kiyasata sayar da shi kan fam miliyan daga Nice a wannan kaka.

Post a Comment

Previous Post Next Post